Wata Mata Dake Garin Gusau Ta Antayama Mijinta Kwalba Ajiki

Rundunarr yan san na jihar Zamfara na tuhumar wata mata mai suna Murjanatu Bilyaminu kan daba wa mijinta kwalba da tayi.

Wannan lamarin ya faru bayan kwana hudu da samun labarin.

Al'amarin ya faru ne a unguwar tudun wada dake Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Dan'uwan mijin, Yusuf Abubakar Maga-yakin Tudunwada ya ce kaninsa na cikin mawuyacin hali sakamakon mummunan rauni da matar ta yi masa wanda kuma ya shafi huhunsa.

Kamar yadda BBChausa ta ruwaito Abubakar ya bayyana yanda abun ya faru da kuma illar da yin hakan ya haifar inda yake cewa;.

"Ita matar tashi ta dauki kwalba, ta fasa masa ita ga kai. Yana dagowa haka sai ta daga masa ita ga kirji, ga gaba wadda yake cewa wurin ya samu rauni mai zurfi.

"Wanda yake cewa idan aka sa kamar dunkulen hannu yana iya shiga cikin jikin shi, har ya zamanto cewa likitoci sun ba mu dama a je a yi mishi x-ray (hoton cikin jiki).

Dalilin da ya sa ta aikata hakan kamar yadda ake hasashen ta shine don mijinta ya hana ta zuwa ofishin yan sanda don ganin halin da dan uwanta ke ciki wanda aka kulle bisa ga wani laifi daban.

"Akwai wani dan'uwanta da ya yi wani laifi (kuma aka tsare shi) ga ofishin 'yan sanda. Sai ya zamanto sun tafi su gane shi don su kai mishi abinci. Suka zo suka gane shi sai suka dawo.

"Wayewar Ranar (Larba) Yau da safe, sai ta ce tana so je ofishin 'yan sandan sai ya ce mata a'a. Kin ga na dawo wurin aiki, zan dan kishingida. Ki bari sai an jima," in ji Abubakar.

Mai magana da yawun rundunar na jihar DSP Muhammed Shehu yace tuni aka kama wanda ake zargin ta aikata hakan kuma lokaci guda aka kai mijin asibiti don ceto rayuwarshi.

Kakakin yace kwamishnan yan sanda na jihar ya bada umarni na a mayar da batun ga sashen binciken manyan laifuffuka don cigaba da bincike.

Yace da zarar an kammala bincike za'a kai kara gaban kotu, Jama'a Sai Muyita Rokon Allah Ya Zabar Mana Abinda Yafi Zama Alkairi.

Share this


0 comments:

Post a Comment