Mutuwar Bilyaminu Ya Tada Zaune Tsaye Da Matarsa Ta Kashe

Safiyar ranar lahadi aka wayi gari da labarin mutuwar Bilyaminu Muhammed Bello wanda matarsa ta daba masa wuka bisa ga zargin cewa yana neman kara aure bayan sakon da ta gani a wayar sa hirar sa da wata.

Bisa ga labarin da wani abokin marigayin mai suna Habib Gajam ya shaida wa manema labarai, Maryam ta amsa laifinta a Asibiti, amma da aka je Caji Ofis sai labari ya sha bam bam, inda yace Maryam tace ita ba ita ta kashe Bilyamin ba, a sanadiyyar fadar da suka yi ne ya yanke da tukunyar shisha, wanda hakan ne yayi sanadiyyan mutuwarsa.

wannan lamarin ya auku bayan shekaran su biyu da yin aure kuma sun samu diya yar wata takwas.
Lamarin dai ya janyo tsegumi a kafafen sada zumunta ta duniyar gizo.

Mawaki wanda ya rera masu wakar bikin su Ali jita bai ji dadin labarin ba inda ya rubuta cewa inda matar tabi nasihohin da yayi mata cikin wakar da yayi masu da lamarin bai faru ba tare da sanya wakar auren su a shafin sa na instagram.

"wish taji wannan nasiha tawa...

Aure lallai tana da dadi kuyi fa'a, sannan hakuri kuyi wa juna, kuyi uzuri....

mata ku guji bincikar wayar mazajanku, kamar yankan albasane, kina scrolling kina hawaye. Namiji fa mijin mace hudu ne, sai kunyi hakuri addini bai hana mu nemaba.

Allah yasa mudace." rubutun da yayi kenan wanda bayan yan mintuna da wallafawa ya cire shi daga shafin sa.
"So sad, wannan azal ne ya fada mata ta aikata wannan mummunar aikin.

ALLAH ka tsare mana imanin mu ka raba mu da mugun ji da mugun gani. Allah ya shirye mu shirin addininin musulunci. Na tausaya masu matuka."

Jaruma Aisha Ahmad Idris ta rubuta a shafin Ali jita yayin da ya wallafa tsokacin sa bisa ga lamarin.

Wasu da dama sunyi tur da aikin da ta tafka yayin da wasu ke ganin laifin rashin tarbiya da ilimin addini ya janyo haka.

Ga tsokacin da sauran mutane suka yi kamar haka;

Wani bawan Allah mai suna Muddassir Kasim yayi la'akari da yadda hirar su zata kasance idan diyar su ta girma kuma tambayi mahaifiyar ta inda inda mahaifin ta yake.

TAMBAYA : Umma Ina babana?

AMSA: yamutu?

TAMBAYA: meya sameshi ?

AMSA: kasheshi akayi..

TAMBAYA: wa ya kasheshi?

TAMBAYA: shin zakice nice?

shin idan ma kin tsalleke hukuncin kisa kingama zaman gidan dankande kinfito zaki Iya yawo cikin yan'uwanki mata?

Shin idan wani ya Kyalla ido ya ce yana sonki yamiki Tambaya shigen wadda diyarki tamiki wace amsa zaki bashi? KASH!!!

Amsar itace zunzurutun

NADAMAAA!!!! Allah yashiryeki yanisantamu da masu Hali irin wannan.

Share this


0 comments:

Post a Comment