Munayin Shafe Shafe Ne Saboda Dalili Biyar (5)
Ba sabon labari bane ganin yadda mata ke adon ban sha'awa da kayan ado na zamani irin su make-up. Mata basu rabuwa da yin ado amma mai ke sanya su yin gyaran fuska da kayan make-up?, 

Ga dalilin nan

"Yan mata adon gari idan babu ku babu gari" kamar yanda muka saba yi masu kirari idan sunyi adon ban sha'awa.

Wannan ado ya kan kawo masu farin jini tare da koma bayan haka kuma na san mafi yawancin mu mukan tambayi junan mu, me ke sa mata yawan sanya make-up?
Ga amsar wannan tamabayar kamar yadda wasu matan suka shaida mana nan kasa:
Dalilai hudu dake sa mata yin gyaran fuska watau make-up

1. yana taimakawa wajen boye kama ko kawar da kurajen fuska
Mafi yawanci babban dalilin dake sanya suna saka make-up shine domin boye kama. Mata na ikirari cewa wasu mazzan na ganin munin su idan basu sanya make-up ba.

2. Yana karfafa takama da nuna izza
Akwai takama da izza dake tare Mace wanda tayi ado kuma ta sanya kayan make-up. Idan ka gan mai haka to ka san cewa ta cika yar kwalisa.

3. Wasu na sanyawa don kawai suna son yin haka
Kamar yanda maza ke son sanya manyan riguna hakazalika mafi yawanci mata ke son sanya make-up.

4. Domin jawo hankalin jama'a da nuna kyau
Babu tantama idan mace ta sanya make-up ta kan jawo hankalin jama'a dake kusa da ita kuma yana sanya mutane suyi mata shaidar kyakyawa.

5. Idan bata sanya ba a tunanin ta adon ta bai cika ba.
Ga wasu abun ya bi jiki domin suna ganin idan basu sanya ba tamkar kamar basu yi ado ban sha'awa.

Mata menene ra'ayin ku game da wannan dalilai da muka lissafo?
Idan akwai dalilin da bamu sanya ba ku gabatar mana a bangaren yin tsokaci.

Share this


0 comments:

Post a Comment