Kissah Daga Shaikh Abdullahi bn Ahmad Al-Mu'azzin

Qissah ce daga Shaikh Abdullahi bn Ahmad Al-Mu'azzin (rah) yace : "Na kasance ina yin 'Dawafi a dakin Ka'abah sai naga wani Mutum (Dattijo) ya Qanqame rigar Ka'abah yana Tsula kuka yana addu'a yana cewa : "YA ALLAH KA FITAR DANI DAGA DUNIYAR NAN INA MUSULMI".

Yana fa'da yana Maimaitawa kuma ba ya Qara komai akan haka. Sai nace masa "Ya Kai Bawan Allah! Shin ba zaka Qara komai akan wannan ba?".

Sai ya juyo gareni yace "Da ache kasan labarina da ba zaka ce haka ba". Sai nace "Menene labarin naka?".

Sai yace "Na Kasance ina da 'Yan uwa Maza guda biyu. Babban cikinsu ya kasance shi Ladani ne (Mai Kiran Sallah). Yayi shekaru Arba'in (40) yana kiran sallah don neman lada. Amma yayin da Mutuwa tazo gareshi sai ya bukaci mu kawo masa Mus'hafi (Wato Alqur'ani cikakke).

Har muna Tsammanin cewa watakil zai yi Tawassuli dashi ne domin neman albarka. Amma yayin da ya karbi Alqur'anin ya rikeshi da hannunsa, Sai muka ji yana Shaidar mana cewa lallai mu zama Shaidu akansa cewar "BABU RUWANSA DA ABINDA KE CIKIN LITTAFIN NAN". (Wato mu shaida cewa ya barranta daga abinda Alqur'ani ya Qunsa).

Nan take ya gama shure-shurensa yana Eehu har ya Mutu kafiri. INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!

Bayan rasuwarsa sai Qaninsa (wato yayana na biyu kenan) ya karbi Ladancin nan yana yinsa har kusan shekaru Talatin (30). Amma shima da yazo mutuwa sai yayi kamar yadda Yayansa ya aikata. (Ya Allah ka kiyayemu daga Mummunan Qarshe).

"To saboda wannan ne nake ta addu'a domin Allah ya tsare min addinina da Imanina in mutum cikin Musulunci".

Sai na tambayeshi "Shin wadannan 'Yan uwan naka (Gasu kamar mutanen kirki) Amma wanne laifi suke aikatawa haka?".

Sai yace "Sun kasance idan sun hau Hasumiyar Masallaci suna kiran sallah, Sukan leqa gidajen Mutane suna kallon al'aurar Matan Mutane da 'Ya'yan Mutane, Kuma suna kallon yima Samari kallo irin na sha'awa".

Domin awancan zamanin babu lasifika. Ladanai sukan hau chan kololuwar hasumiya ne idan zasu kira sallah. Don haka suke iya kallon cikin gidan kowa, da wuraren wanka da sauran haramtattun abubuwa.

Na kawo wannan ne domin jan hankalin Matasa Masu shiga gidajen Mutane suna kallon al'aurorin Mata, da masu Qura ido suna yima 'Ya'yan Mutane kallon sha'awa, da Kuma Injiniyoyi masu hawa kan Pal-Waya ko Qarafun Service na gidajen waya, da Magina da Kafintoci da Masu Fenti masu hawa saman gidaje domin gudanar da aiki.

Hakanan masu shiga shafukan Internet domin kallon al'aurori da Zinace-zinace, da 'Ya'yan Musulmai masu bude shafukan batsa din ha'bbaka alfasha atsakanin al'ummah.. Da Mata masu Kalle-kallen haramun wai don biyan sha'awarsu, da masu bude Groups na batsa a Facebook da Whatsapp (Mata da Maza).

Duk wanda bai ji tsoron Allah ba, Allah ba zai, ji tsoron azabtar dashi ba. Duk wanda bai ji kunyar Allah ba, Allah ba zaiji kunyar azabtar dashi ba. Wanda yaga zai dena ya dena. Wanda yaga ba zai dena ba, to gashi nan ga duniyar..

Ranar Mutuwarka ma ta isheka fargaba.. Kwanciyar Qabari ma ta isheka nadama.. Ranar hisabi ma ta isheka tonon asiri!!.

Zauren Fiqhu ya rairayo wannan Qissar ne daga littafin 'Alamatu Husnil Khatimah. Da fatan Allah yasa wannan gargadi ya shiga zukatanmu baki daya. Allah ya kyautata karshenmu yasa mu cika da imani.

Don Allah ku tayamu wajen ya'da wannan Da'awar domin samun lada garemu baki daya.

Share this


0 comments:

Post a Comment