Karanta Yadda Maryam Sanda Ta Kashe Mijinta Saboda Zafin Kishi

Kakakin hukumar Anjuguri Manzah ya tabbatar da lamarin kana ya kara da cewa sun kama wasu wadanda suke zargin cewa sun taimaka wajen aikata laifin.

Rundunar yan sanda na Abuja ta gano bidiyon yanda abubuwa suka kasance kafin mutuwar Bilyaminu Muhammed Bello, daya daga cikin yaran tsohon shugaban jam'iyar PDP Halliru Bello.

Bisa ga labarin da abokin marigayi mai suna Habib Gajam ya fitar, Maryam ta amsa laifin aikata laifin yayin da aka tafi asibiti amma da aka tafi ofishin yan sanda lamarin ya canja inda take zargin cewa tukuyar shisha tayi sanadiyar mutuwar sa bayan wata yar rigima da suka yi.

Matar ta daba masa wuka sau uku a baya kana ta kara wani a kirjin sa wanda kuma daga bisani ta kaishi asibiti da kanta, kamar yadda abokin marigayin ya fada.

Maryam wanda har yanzu tana nan tsare a ofishin jami'an tsaro ta musanta zargin cewa ita ta kashe mijin ta.

" Wallahi Ko Kadan Ban Yi Niyyar Kashe Masoyina Uban 'Yata Ba, Sharrin Shaidan Ne" kamar yanda tace kafin hukuma ta fara bincike akan ta.

Yayin da ta shiga hannun jami'an tsaro labarin ya canja zuwa "Ba Ni Na Kashe Mijina Ba, Tukunyar Shisha Ce Ta Yi Masa Mummunar Rauni A Lokacin Da Muke Fada".

Dangane da binciken da suke kan lamarin, hukumar yan sanda tace ta gano wani bidiyon a gidan Bilyaminu wanda ke nuna yanda abubuwa suka kasance kafin mutuwar sa kuma ta kama masu tsaron gidan.

Kakakin hukumar Anjuguri Manzah ya tabbatar da lamarin kana ya kara da cewa sun kama wasu wadanda suke zargin cewa sun taimaka wajen aikata laifin.

Labarin mutuwar Bilyaminu ya jawo tsegumi a kafafen sada zumunta, akasarin mutane na son hukuma ta yanke hukunci da ya kamata.

Gaskiya Jama'a Lahira Akwai Bayani Dan Allah Ka/Ki Daure kuyi share Ta Hanyar Taba Kan Share Bottom A Nan Kasa Mungode.

Share this


0 comments:

Post a Comment