Jirgin Kasa Yayi Barna a Jahar Legas Dake Najeriya

TTashin hankali da ba’a sa masa rana! Rahotanni sun kawo cewa mummunan hatsarin jirgin kasa ya afku jihar Lagas.

Al’amarin ya afku ne a garin Agege dake jihar inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Hatsarin dai ya faru ne ta sanadiyar kauce hanya da jirgin yayi daga kan kwangiri a safiyar yau Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Olarinde Famous-Cole ya tabbatar da afkuwar al’amarin, in da ya kara da cewa, jirgin ya kuma ci karo da wata katuwar motar daukan kaya.
Famous-cole ya ce, a yanzu haka, an tura jami’an tsaro wurin da hatsarin ya faru amma bai bada alkaluman mutanen da suka mutu ba.

Ba a karon farko kenan ba da ake samun hatsarin jirgin kasa a garin Agege mai cike da hada-hadar jama’a.

Share this


0 comments:

Post a Comment