Fitaciyar Jarumar Nollywood Linda Osifo Tana Son Tayi Film Da Rahama Sadau

Fittaciyar jarumar masana'antar nollywood dake kudancin kasar Linda Osifo ta bayyana kudirin yin wasa tare da jarumar hausa Rahama Sadau.
Jarumar tace Rahama Sadau yar fim ce wanda ke cike da basira kuma ta kware sosai a fannin.

Ta bayyana haka yayin da kawo mana ziyara ta musamman makon da ya gabata.

Linda Osifo tace fitowar wasu jaruman kannywood a fina-finan nollywood yana taimaka wajen bunkasa masana'antar shirya fim na kasar baki daya.

Jarumar wanda tayi fice a fina-finai daban daban na dandalin nollywood tace hakika jaruman Kannywood na cike da basira kuma nan ba da dadewa tana fatan zata yi aiki da wasu daga cikin su.

Linda wanda asali yar kabilar Ishan ce dake nan jihar Edo tace zata so ta koyi yaren hausa domin yana cikin yarurruka da take neman iyawa A Duniya.

Share this


0 comments:

Post a Comment