Buhari yayi dana sani, ficewar Atiku daga jam'iyar APC ( Karanta Cikaken Kabari Nan )


Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nadamar ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daga jam'iyar APC yayin da yake jawabi a fadar sa na Villa ranar litinin 27 ga watan Nuwamba.

Shugaban ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da kwamitin mutum 30 da zasu yi binciken kan albashin ma'aikatan kasar ranar litinin. Yayi ma shugaban jam'iyar APC John Odigie-Oyegun jaje game babban reshin da jam'iyar tayi ficewar daya daga cikin j masu ruwa da tsaki da jam'iyar Atiku.

"Ina mai mika sakon jaje ga jam'iyar mu game da babban rashi da ta samu na rasa daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyar" Yace.
Ficewar Atiku daga APC

Ranar juma'a 24 ga watan Nuwamba tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya mika takardan murabus daga jam'iyar. A cikin takardar Atiku yana zargin shugaba Buhari da yin watsi dashi kana ya kushe jam'iyar inda yake zargin ta da aikata ayyuka wadanda suka saba ma tsarin dimokradiya.

Game da murabus da yayi jam'iyar adawa ta
PDP ta bukace shi da ya sauya sheka zuwa jam'iyar wanda tayi sandiyar shi zaman mataimakin shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2007.

Shima gwamnan jihar kaduna Malam Nasir El-rufai yayi tsokaci game ficewar sa inda yake cewa Babu wanda yake da farin jinin shugaba Buhari.

Duk da cewa Atiku bai bayyana jam'iyar da zai sauya sheka zuwa ko kuma zai fito takara a zaben 2019, ana sa ran cewa zai bayyana anniyar sa karkashin jam'iyar PDP ganin yanda yake ta ganawa da jiga-jigan jam'iyar cikin sirri.

Ni Marubucin Wannan Labari Na Kan CE Allah Ya Zabar Mana Abinda yafi Zama Alkairi Amin Sunnah Amin

Share this


0 comments:

Post a Comment