Abin Mamaki Ali Nuhu Ya Angonce Da Hadiza Gabon

A cikin wani sabon shirin fim jaruma Gabon ta fito a matsayin matar shi,
Fitaccen jarumi kuma babban direkta fina-finan hausa na masana'antar Kannywood Ali Nuhu ya musanta jita-jita dake yaduwa na cewa ya auri jaruma Hadiza Gabon a asirce bisa ga hoton su dake yawo a kafafen sada zumunta.

Hoton wanda jama'a ke tsegumi akan shi an dauke shine yayin da suke shirya wani sabon fim mai suna "Akushi".

A cikin shirin jaruma Gabon ta fito ne a matsayin matar shi.

"Sarkin kannywood" kamar yanda aka yi mai lakabi yayi kira ga jama'a da su daina yada jita-jita wanda bai da asali.

A matsayin su na yan fim ire-ire hotunan da suka dauka zai cigaba da fitowa don inganta shirirn fim da suke neman fitar domin nishadantar da masu bibiyan fina-finan Hausa Film.

Share this


0 comments:

Post a Comment